Ta ce bangaren Sin ya bukaci bangaren Isra'ila da kada ya yi duk wani yunkurin da zai kawo tashin hankali da dagula maido da shawarwari tsakanin Palasdinu da Isra'ila.
Madan Hua ta ce, kamata ya yi Isra'ila ta dauki matakan da suka dace na sake maido da fahimtar juna da Palasdinu kana ta dauki kwararan matakan da za su ciyar da shirin wanzar da zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya gaba tare da tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a shiyyar baki daya.
Kasar Isra'ila dai na ci gaba da fuskantar matsin lambar diflomasiya daga al'ummomin kasa da kasa dangane da shirinta na gina gidaje 3,000 a yammacin kogin Jordan da gabashin birnin kudus da kuma yankunan nan na E1 da suka hade wuraren biyu. (Ibrahim)