Ehud Barak ya yi bayani kan shirin ga maneman labarai, inda ya nuna cewa, hukumar ikon mallakar al'ummar Falesdinu za ta tafiyar da harkokin wasu Yahudawan da ba su so su janye jiki ba.
Manyan jami'ai masu tsattsauren ra'ayi na kasar Isra'ila da dama sun kai suka ga wannan shawarar da Ehud Barak ya gabatar game da janye jiki a gefe daya, kuma 'yan siyasa cikin gida na kasar su ma sun nuna kiyayya bisa dalilin cewa, Isra'ila ta taba janye jiki daga zirin Gaza a gefe daya a shekara ta 2005, amma hakan bai taimaka wajen ingiza huldar sulhuntawa tsakanin Falesdinu da Isra'ila ba.
A watan Mayu na shekarar da ake ciki, Ehud Barak ya taba bayyana ra'ayinsa game da janye jiki a gefe daya yayin da yake yin jawabi ga jama'a a fili, shi ma ya gamu da zargin da Palestinu ta yi masa. Bangaren Falesdinu na ganin cewa, janye jiki a gefe daya ba za ta taimaka wajen cimma burin kasashen biyu ba, sai ma dai zai hadassa karin rashin jituwar da ke tsakaninsu.(Maryam)