Yayin da ministan kula da harkokin gidaje da gine-gine na Isra'ila Ariel Atias ke zantawa da manema labaru, ya bayyana cewa, Isra'ila ta dauki wannan mataki bayan da aka zartas da kudurin shigar da Falesdinu cikin hukumar kula da harkokin ilmi, kimiyya da al'adu na M.D.D UNESCO.
Haka kuma, a ranar 31 ga watan Oktoba, a gun taron UNESCO, an zartas da kudurin shigar da Falesdinu cikin kungiyar, nan take, Isra'ila tana nuna adawa ga wannan mataki da kakkausan harshe, kuma firaministan kasar Netanyahu ya ba da umurnin kara saurin gina matsugunan a yankunan gabashin birnin Kudus da yammacin gabar kogin Jordan, don yin kashedi ga Falesdinu.
Kana, jami'an Amurka sun yi kushe daukar wannan mataki da Isra'ila ta yi da cewa, ba zai amfana ba wajen warware batun Falesdinu da Isra'ila da kawo sassauci ga yunkurin samar da zaman lafiya a yankin Gabas ta tsakiya.(Bako)