A ran 22 ga wata, majalisar dokokin kasar Isra'ila ta zartas da wata doka, inda aka tanadi cewa, dukkan kudurori kan janye jiki daga birnin Kudus na gabas da tudun Golan ba za su taka rawa ba sai dai suka samu kuri'u masu goyon baya da yawansu ya zarce kashi 2 cikin kashi 3 a cikin majalisar, in ba haka ba za a nemi shirya aikin jefa kuri'ar raba gardama a kansu.
Kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin Hong Lei ya bayyana a ran 26 ga wata, cewar wannan dokar da kasar Isra'ila ta zartas ba ta dace da kudurorin MDD da abin ya shafa ba. Kana kuma sakamakon dokar kawai, ba za a musanta wani hakikanin abu kan cewa ba, birnin Kudus na gabas da tudun Golan yankuna ne na kasashen Larabawa. (Kande Gao)