A wannan rana, M.D.D ta shirya wata muhawara game da batun yankin Gabas ta tsakiya, yayin da Li Baodong ke yin jawabi, ya ce, yanzu, an shiga halin kunci a yunkurin samar da zaman lafiya a yankin Gabas ta tsakiya, kuma Sin ta nuna damuwa sosai game da batun, kuma kasar Sin ta bukaci bangarorin da abin ya shafa da su bayyana anniyarsu ta siyasa, kuma a warware rikici tsakanin Falesdinu da Isra'ila ta hanyar diplomasiyya, don cimma burin zaman jituwa cikin lafiya tsakanin Falesdinu da Isra'ila.
Li Baodong ya ce, Sin ta kasance daya daga cikin kasashen da suka fara amince da kasar Falesdinu tun da wuri, kuma kullum Sin ta kan nuna goyon baya ga sha'anin kafa kasar Falesdinu cikin 'yanci, kuma Sin ta nuna goyon baya ga shigar da Falesdinu cikin M.D.D.(Bako)