in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Isra'ila na shirin sake kafa matsugunai a gabashin birnin kudus
2011-09-28 15:01:48 cri

Kwanan baya, ma'aikatar harkokin cikin gida ta kasar Isra'ila ta zartas da shirin kafa matsugunan Yahudawa 1100 a gabashin birnin Kudus. A game da haka, kasar Amurka ta nuna rashin jin dadi, ta kuma bayyana cewa, hakan zai kawo illa ga shawarwarin shimfida zaman lafiya a tsakanin bangarorin Isra'ila da Palesdinu.

Kakakin ma'aikatar gudanarwa ta kasar Amurka Victoria Nuland ta furta hakan ne a gun taron manema labaru da aka yi a ran 27 ga wata. Ta ce, kasar Amurka ta dade tana kalubalantar bangarori biyu da kada su yi aikin da zai kawo barazana ga huldarsu, kasar Amurka tana iyakacin kokarin ta wajen ganin an farfado da shawarwari tsakanin bangarorin biyu.

Bangaren Palesdinu ya yi Allah wadai da shirin Isra'ila na gina matsugunai a gabashin birnin Kudus.

A wasu kwanaki kafin Isra'ila ta gabatar da shirin gina sabbin matsugunai, MDD da kasar Amurka da kungiyar tarayyar kasashen Turai da kasar Rasha sun bayar da sanarwa a ran 23 ga wata a hedkwatar MDD cewa, za su yi kokarin farfado da shawarwarin shimfida zaman lafiya a tsakanin bangarorin biyu cikin wata daya, kuma za a samu sakamako mai yakini a cikin watanni 6 masu zuwa, kuma za a yi kokarin kulla yarjejeniya kafin karshen shekarar 2012.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China