Kakakin rundunar sojoji ta JTF da ke jihar Borno Musa Sagir ya bayyana cewa, wadannan mahara biyu sun yi shirin kai hari ne ga ayarin motoci a kasuwar Gambaru da ke da nisan mita 100 da hanyar Gambaru-Gala a birnin Maiduguri.
Ya ci gaba da bayyana cewa, mahara 2 sun mutu ne sakamakon harin da suka kai, amma babu wasu mutanen da suka mutu ko jikkata cikin harin bom din.
Bai kai wata guda ba da wasu shugabanni na kungiyar Boko Haram suka sanar da daina kai hare-hare a kasar, amma harin da aka kai a ranar Jumma'a da ma sauran hare-haren da aka fuskanta a kasar sun nuna cewa, kila ma, akwai wasu 'yan kungiyar da ba su amince da daina kai harin ba.
Birnin Maidugiri ya zamo waje da ke fama da harin kungiyar Boko Haram a kasar Nijeriya, kuma gwamnatin kasar ta sanar da dokar hana fitan dare, a lokuta da dama sakamakon hare-haren da aka samu a shekarar bara.(Bako)