Mazauna unguwar sun ce 'yan bindiga da ake kyautata zaton 'yan kungiyar Boko Haram ne sun mamaye ofishin yanki na 'yan sanda dake hanyar Baga, ranar Alhamis da dare inda suka yi ta wurga ababai masu fashewa a ofishin wanda a shekarar 2011 kungiyar ta yi yunkurin lalatawa.
Mai magana da yawun hukumar 'yan sanda a jihar Borno Gideon Jibril ya tabbatar da aukuwar lamarin ga kamfanin dillancin labaran kasar Sin, Xinhua.
Ya ce 'yan bindigar sun yi kokarin kai hari a ofishin 'yan sandan to amma jami'an tsaro na hadin gwiwa da 'yan sanda sun hana su cimma nasarar gudanar da wannan danyen aiki.
Gideon ya ci gaba da cewa masu harin da dama sun rasa rayukansu yayin musayar wuta ko da yake ba zai iya bada cikakken bayani kan yawan wadanda suka mutu ba.
Shi ma mai magana da yawun hukumar ba da agajin gaggawa ta kasar Najeriya NEMA Abdulkadir Ibrahim ya ce an samu aukuwar fashewar bama bamai a daren Alhamis da kuma safiyar Juma'a, to amma ya bayyana wa kamfanin dillancin labaran kasar Sin Xinhua cewar ba shi da masaniya ko akwai wadanda suka mutu ko kuwa a'a.
Mazauna garin da dama sun yi imanin cewa a kalla bama bamai kusan 23 ne suka fashe a cikin garin sannan an dade ana musayar wuta tsakanin jami'an tsaro da 'yan kungiyar Boko Haram. (Lami Ali)