Cikin wata sanarwar da kamfanin dillancin labarun kasar Sin Xinhua, ya samu a ranar Asabar 9 ga wata, shugaba Jonathan ya mika jajensa ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu, yana mai alkawarin cewa, sadaukarwar da ma'aikatan suka yi, za ta haifar da sakamako mai amfani, duba da yadda gwamnatin kasar ta zage dantsen ganin an cimma burin dakile wannan cuta ta shan inna daga dukkanin fadin kasar, aikin da wadanda suka rasun suka baiwa cikakkiyar gudummawa.
Shugaban ya tabbatarwa al'ummar kasar, da ma 'yan kasashen waje dake kasar, musamman ma kungiyoyin kasa da kasa masu kula da aikin jinya, da takwarorin Najeriyar cewa, irin wannan ta'asa da 'yan ta'adda ke aikatawa ba za ta hana gwamnatinsa ci gaba da kokarin rage yawan mace-macen kananan yara da masu juna biyu da ake yi, a dukkanin fadin kasar ba.
Haka zalika, a cewar shugaba Jonathan, gwamnatinsa za ta ci gaba da iyakacin kokarinta, don ganin an cafke 'yan ta'addan, kana ya ba da umarnin karfafa matakan tsaro, a wuraren da ma'aikatan jinya ka iya gamu da makamancin wannan hari. (Bello Wang)