in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
'Yan bindiga sun kashe mutane 10 a yankin tsakiyar kasar Najeriya in ji 'yan sanda
2013-02-23 17:11:37 cri
Wani mai magana da yawun 'yan sanda ya bayyana ranar Jumma'a cewa wasu 'yan bindiga da ba'a san ko su wanene ba sun kashe a kalla mutane 10 a wani kauyen jihar Plateau dake tsakiyar Najeriya.

Mai magana da yawun hukumar 'yan sanda a jihar John Onuigbo ya tabbatarwa kamfanin dillancin labaran kasar Sin, Xinhua aukuwar wannan lamari a Jos, babban birnin jihar, inda ya ci gaba da cewa mutane 10 da ake ganin iyali daya ne an kashe su a daren Alhamis da bindiga a kauyen Kogom dake gundumar Vwang a cikin karamar hukumar Jos ta kudu a jihar Plateau.

Ya ci gaba da cewa 'yan sanda na ci gaba da binciken lamarin to amma ya kara da cewa ba'a kama kowa ba dangane da wannan lamari,

Daya daga cikin wadanda suka tsallake rijiya da baya yayin harin 'yan bindigar, Habila Musa ya bayyanawa Xinhua cewa masu harin suna sanye da kayan sojoji kuma sun shafe awa daya suna harbi.

Mai magana da yawun gwamnan jihar Ayuba Pam wanda shi ma dan asalin yankin da aka kai harin ne ya ce wannan hari abin yin Allah wadai ne ya kuma jaddada cewa gwamnati za ta ci gaba da kokarin tabbatar da zaman lafiya a jihar.

Pam ya bayyanawa Xinhua cewa jami'an tsaro sun kira shi ta waya inda suka bayyana masa cewa an kai hari a kauyen Kogom kuma mutane 10 sun mutu.

Wani basaraken kauye ya yi tir da wannan hari inda ya yi kiran a janye jami'an tsaro na hadin gwiwa daga jihar tare da zargin cewa Fulani ba za su iya kawo irin wannan hari ba. (Lami Ali)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China