Mai magana da yawun hukumar 'yan sanda a jihar Musa Majia ya bayyanawa kamfanin dillancin labaran kasar Sin Xinhua cewa, 'yan bindigan sun taho ne kan babur mai kafa uku inda nan take suka harbe mata uku a unguwar Fijin Kashu, suka kuma raunata wasu guda uku.
Haka kuma wata kungiyar ta 'yan bindiga ta kai hari a cibiyar lafiya dake Hayen Hotoro, inda nan take suka bindige mata guda shida dake aikin raba rigakafin ciwon inna a jihar ta arewacin Najeriya.
Majia ya kara da cewa, zuwa yanzu dai babu wanda aka cafke, to amma jami'an tsaro sun zagaye unguwannin, daga nan bai bada wani karin bayani ba.
Kwamishinan lafiya a jihar kano Abubakar Labaran shi ma ya tabbatar da kisan tare da nuna matukar bakin ciki dangane da lamarin. Yana mai bayyana cewa, ko shakka babu wannan abin bakin ciki ne ganin yadda 'yan bindigar suka kai hari kan mutane dake aikin kawo ci gaban jihar. (Lami Mohammed)