in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babban Sifeton 'yan sandan Nigeria ya umarci baiwa ma'aikatan lafiya tsaro na musamman
2013-02-11 16:26:16 cri
Babban sifeton rundunar 'yan sandan Nigeria Muhammed Abubakar, ya yi umarnin bada tsaro na musamman ga dukkanin ma'aikatan lafiya, dake gudanar da ayyukan riga kafin shan inna, wanda ke ci gaba da gudana a halin yanzu.

Wata sanarwa data fito daga ofishin babban sifeton 'yan sandan tace, daukar wannan mataki ya biyo bayan harin da aka kaiwa wasu likitoci 'yan asalin kasar Korea ta arewa su 3, da sanyin safiyar ranar Lahadi 10 ga watan nan, a garin Potiskum na jihar Yobe, wadda ke Arewa maso Gabashin kasar. Harin da kuma nan take ya sabbaba mutuwar likitocin.

Sanarwar ta kara da cewa wannan shiri na bada tsaro zai hada da ragowar likitoci dake ayyukan kula da lafiya na musamman.

A ranar Juma'ar data gabata ma dai wasu 'yan bindiga sun hallaka wasu mata su 9, dake aikin bada allurar ta Polio, yayin wasu hare-hare da aka kaiwa tawagar ma'aikatan a jiahar Kano dake Naijeriyar. (Saminu Alhassan Usman)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China