in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yan sandan Najeriya sun sha alwashin cafko wadanda suka kashe jami'ai
2013-05-10 10:13:34 cri
Mahukuntan ‘yan sandan Najeriya sun yi alkawari ranar Alhamis din nan na yin iyakacin kokarinsu don tabbatar da ganin sun cafko dukkan wadanda suke da hannu a kisan ‘yan sanda a jihar Nassarawa dake tsakiyar arewacin kasar. Mai magana da yawun hukumar ‘yan sanda na kasa, Frank Mba, cikin wata sanarwar da kamfanin dillancin labaran kasar Sin, Xinhua ta samu a Abuja, na mai bayyana cewa, wajibi ‘yan sanda su kawo karshen wannan lamari na take doka. Ya ce, speto janar din ‘yan sanda ya umarci dukkan kwamandoji da sassa, har ma da mataimakan speto janar din ‘yan sanda gami da kwamishinoni, da su yi amfani da karfi da karfe wajen tabbatar da cewa, an kawo karshen ta’addanci da karya doka a kasar. Mai magana da yawun hukumar ‘yan sandan ya bayyana kisan da aka kai wa jami’an ‘yan sanda a matsayin abu mai ta da hankali da sa bakin ciki. Ya ci gaba da cewa, an fuskanci irin hakan a jihar Bayelsa dake kudancin kasar, da kuma jihar Borno dake arewa maso gabashin kasar, inda ya ce, wannan al’amari ya bullo da wata sabuwar barazana ga aikin samar da tsaro a kasar.(Lami)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China