Mahukuntan jihar Nasarawa a tarayyar Najeriya sun tabbatar da rasuwar sama da 'yan sanda 20, a kauyen Atakio dake jihar ta Nasarawa, bayan da wasu mahara 'yan kungiya mai suna Ombatse suka kai farmaki kan su, lokacin da suke tsaka da gudanar da ayyukansu a ranar Laraba 8 ga watan nan.
Yayin zantawarsa da 'yan jaridu a babban birnin tarayyar Najeriya Abuja, gwamnan jihar ta Nasarawa Umaru Al-Makura ya ce, dama a baya ma wadannan 'yan tada-zaune-tsaye, sun sha ta da hankulan al'umma, tare da barazana ga yanayin tsaron jihar, duka da nufin yiwa gwamnatin jihar mai ci kafar-ungulu.
Gwamna Al-Makura dake birnin tarayya Abuja, domin ganawa da mataimakin shugaban kasa Namadi Sambo kan lamarin, ya bayyana takaicinsa, ganin yadda 'yan kungiyar ke tilastawa 'yan kabilarsu shiga wannan mummunar ta'ada ta tada-zaune-tsaye.
Daga nan sai ya jaddada aniyar gwamnatinsa ta daukar dukkanin matakan duk da suka dace, wajen dakile ayyukan wannan kungiya. Har ila yau Al-makura ya yi alkawarin taimakawa iyalan wadanda wannan balahira ta aukawa.(Saminu)