A Damaturu, babban birnin jihar Yobe a arewa maso gabashin Nigeriya, a kalla mutane 25 ne suka hallaka, ciki har da 'yan sanda da maharan a ranar Alhamis din nan lokacin wata bata kashi tsakanin sojoji da wassu masu dauke da makamai a garin Gashua dake karamar hukumar Bade, a bayanin da rundunar 'yan sanda suka fitar wanda kamfanin dillancin labaran kasar Sin Xinhua ya samo mana.
Kwamishinan 'yan sandan jihar Sanusi Rufai wanda ya tabbatar da adadin wadanda suka rasu ga manema labarai ya ce, a cikin su, akwai 'yan sanda 5 da masu dauke da makamai 20 a lokacin wannan bata kashin da ya kwashe tsawon awoyi da dama.
Malam Rufa'I ya kuma tabbatar da cewa, wassu 'yan sanda 2 sun samu rauni a lokacin da wassu mahara suka tilasta ma wani manajn banki bude babban asusun da aka ajiye makudan kudade, suka kuma kwashe kudi mai yawan gaske, sannan suka arce da motoci biyu na bankin kirar Fijo 406 da Toyota Corolla.
An samu bindigogi biyu kiran hannu da bindiga mai dogon zango da kuma gurneti na hannu guda 19, sai wassu bindigogi nau'i daban daban daga hannun maharani, inda aka kama daya daga cikin maharan kuma yanzu haka yana tsare, ana masa tambayoyi.
Babban jami'in 'yan sanda ya ce, wadannan kungiyar ne ke amfani da kayan 'yan sanda da na soji suna kai hari, suna kuma ta da hankalin jama'a a garuruwan a cikin lokutan nan.
Jihohin Yobe da Borno dai duka a arewa maso gabashin kasar Nigeriya suna fama da tashin hankali tsakanin 'yan bindaga da jami'an tsaro, inda a makon da ya gabata ne aka yi shigen irin wannan bata kashi wanda ya yi sanadiyar hallakar mutane 185.(Fatimah)