Sojojin Najeriya sun bayyana cewa, sun kashe wani kwamandan kungiyar Boko Haram mai suna Mohammed Chad a ranar Asabar a garin Maiduguri da ke arewa maso gabashin Najeriya yayin wani samamen hadin gwiwa da jami'an tsaro suka gudanar.
Kakakin rundunar tsaro ta JTF Laftanar kanar Sagir Musa ne ya bayyana hakan, cikin wata sanarwa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua na kasar Sin ya samu kwafe cewa, Chad yana da hannu a hare-haren ta'addanci da dama da aka kai a jihar Borno da sauran jihohin kasar a baya.
Ya ce, dakarun rundunar ta JTF da jam'in tsaron farin kaya na SSS ne suka kai wani samame na musamman a unguwar Ruwan-Zafi da ke garin na Maiduguri, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar kwamandan da ake yiwa lakabi da Mohammed Chad, haifaffen garin Marte da ke jihar ta Borno, kana mutumin da ke cikin jerin sunayen da JTF din ke nema ruwa a jallo.
Garin Maiduguri da ke arewa maso gabashin Najeriya, ya kasance tungar kungiyar ta Boko Haram da gwamnatin Najeriya ta sanya tare da sassauta dokar ta bacin da ta sanya sakamakon hare-haren da ake kaiwa. (Ibrahim)