in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Najeriya ya tsai da ziyarar aiki a waje saboda matsalar tsaro
2013-05-10 09:50:31 cri

Shugaban kasar Najeriya Goodluck Jonathan ya katse ziyarar da yake a kasar Afirka ta Kudu da fasa kai ziyara a kasar Namibiya, wadda ya fara a ranar Alhamis.

Wata sanarwa daga jami'in watsa labaran shugaban da ofishin kamfanin dillancin labaran kasar Sin, Xinhua, ta samu a Abuja na nuni da cewa, shugaban zai dawo Abuja ba tare da jinkiri ba domin shawo kan matsalar tsaro a jihohin Borno, Plateau da Nassarawa.

Mutane da dama, ciki har da jami'an tsaro sun rasa rayukansu sakamakon harin da kungiyar Boko Haram ta kai a cibiyoyin soji da na tsaro, gidan kaso da kuma barikin 'yan sanda da na soja a jihar Borno a ranar Litinin.

Bayan isowar tasa, shugaban Jonathan ya gana da hafsan soji, da shugabannin kafofin soji, speto janar din 'yan sanda da kuma shugabannin sassa na tsaro da nufin yin nazarin lamarin tsaro a kasar. (Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China