in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wani hari ya hallaka mutane 55 a garin Bama dake jihar Borno a Najeriya
2013-05-08 10:44:04 cri

Rahotanni daga jihar Borno dake arewa maso gabashin Najeriya, na nuna cewa, a kalla mutane 55 sun rasa rayukansu, yayin da wasu mahara da ake zaton 'yan kungiyar nan ta Boko Haram ne suka kai farmaki kan wasu gine-ginen jami'an tsaro a garin Bama, mai tazarar kilomita 187 daga Maiduguri, babban birnin jihar ta Borno.

An ce, maharan da yawansu ya kai 200 sun kai sumamen ne da sanyin safiyar ranar Talata 7 ga watan nan sanye da kayan soji, cikin wasu motoci guda biyu, suka kuma bude wuta da manyan bindigogi kan barikin soji, mai kunshe da bataliya ta 202 dake garin na Bama, sun kuma kai wani farmakin kan jami'an tsaron gidan yarin dake yankin, da kuma wani ginin ofishin 'yan sanda, da barikin 'yan sandan, da sakatariyar karamar hukumar ta Bama, da kuma ginin wata kotun majistare, wadanda suka cinnawa wuta.

A tabakin jagoran rundunar hadin gwiwar JTF a jihar Laftanar kanal Sagir Musa, an harbe mahara 10 nan take, yayin da su ma wasu sojoji biyu suka rasa rayukansu. Baya ga wadannan mutane, Sagir ya ce, harin na ran Talata ya yi sanadiyar rasuwar jami'an tsaron gidan yari su 14, lamarin da ya baiwa wasu fursunoni 105 samun damar arcewa. Har wa yau, harin ya hallaka wasu 'yan sanda 22, yayin da wasu yara kanana 3, da wata mace guda suka kone kurmus.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China