Mahukunta a Nigeria sun ce, ba za su yanke hukunci kan halin da 'yan kasashen wajen nan su 7, da aka yi garkuwa da su ke ciki ba, duk kuwa da sanarwar da kungiyar Ansaru ta bayar na kashe mutanen.
Minista a ma'aikatar harkokin wajen kasar ta Nigeria Olugbenga Ashiru ne ya bayyana wa manema labaru hakan, ranar Talata 12 ga watan nan a
birnin Abuja. Ministan ya kara da cewa, wajibi ne a samu shaidu na hakika, kafin tabbatar da mutuwar mutanen. Wannan dai tsokaci na zuwa ne kwana guda, bayan da ministan ma'aikatar harkokin cikin gidan kasar Abba Moro, ya ce, kawo wannan lokaci kisan mutanen lamari ne da ba a tabbatar da shi ba.
Idan dai ba a manta ba, a ranar Juma'ar da ta gabata ne kungiyar 'yan kaifin kishin Islama ta Ansaru dake Nigeria, ta bayyana cewa, ta kashe 'yan kasashen wajen su 7, dake aiki da wani kamfanin gine-gine mai suna Setraco, dake jihar Bauchi a arewa maso gabashin kasar.
Haka nan kungiyar ta ce, ta kashe mutanen ne, sakamakon yunkurin ceton su da jami'an tsaron kasar ta Nigeria da na Birtaniya suka yi.(Saminu)