Shugaban Najeriya Dr. Goodluck Jonathan, ya yi tir da harin ta'addanci da wasu 'yan bindiga suka kai garin Bama, dake arewa maso gabashin Najeriya ranar Talatar da ta gabata, harin da nan take ya sabbaba rasuwar mutane kimanin 55.
Shugaba Jonathan ya kuma ja kunnen masu burin ta da zaune tsaye, yana mai cewa, bai dace a kalli batun sulhu da gwamnati ke burin aiwatarwa, tamkar wani nau'in gazawa ba.
Wata sanarwa da mai taimakawa shugaban ta fuskar yada labaru Reuben Abati ya fitar, ta rawaito shugaba Jonathan na cewa, ci gaba da kai hare-hare makamantan wadanda suka auku a garin na Bama, tamkar yiwa shirin wanzar da zaman lafiya da gwamnati ke kokarin aiwatarwa a arewacin kasar karan-tsaye ne. Daga nan sai ya jajantawa iyalan jami'an tsaron da suka rasa rayukansu sakamakon wannan hari.
A ranar Talata 7 ga watan nan ne dai rundunar soji da ta 'yan sandan kasar ta Najeriya suka tabbatar da kisan mutane kimanin 55, sakamakon taho-mu-gama da jami'an tsaro suka yi, da wasu mahara da ake zaton 'yan kungiyar nan ta Boko Haram ne a garin na Bama, mai nisan kilomita 187 daga garin Maiduguri, babban birnin jihar Borno dake arewa maso gabashin Najeriyar, jihar da a baya ta sha fama da hare-hare masu alaka da kungiyar Boko Haram.(Saminu)