Firaminista Li ta bayyana hakan ne a yau Talata 23 ga wata a birnin Beijing, fadar gwamnatin kasar.
Bisa kididdigar da hukumar kula da harkokin jama'ar lardin Sichuan ta yi, an ce, ya zuwa karfe 6 na safiyar ranar 23 ga wata, mutane 193 sun rasa rayukansu a sakamakon girgizar kasa mai karfi maki 7 da ta abku a garin Lushan dake lardin Sichuan, mutane 25 sun bace, sannan kuma mutane 12211 sun ji rauni. Kana mutane fiye da miliyan 1.99 suna fama da bala'in.
Haka kuma, bisa kididdigar da ofishin bada umurni na hukumar 'yan kwana-kwana ya yi, an ce, ya zuwa karfe 8 na safiyar ranar 23 ga wata, an ceci mutane 165 da suka gamu da bala'in, guda 150 a cikinsu sun tsira da ransu. Kana an kaura jama'a 6976 zuwa wurin daban. A halin yanzu, ana ci gaba da yin aikin bada ceto a yankin dake fama da bala'in. (Zainab)