in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yawan mutanen da suka rasu sakamakon bala'in girgizar kasa a gundumar Lushan da ke lardin Sichuan na kasar Sin ya karu zuwa 193
2013-04-23 16:44:43 cri

Bisa kididdigar da hukumar kula da jin dadin jama'a ta lardin Sichuan ta kasar Sin ta bayar, an ce, ya zuwa safiyar yau talata 23 ga wata, bala'in girgizar kasa da karfinsa ya kai maki 7 na gundumar Lushan ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 193, sannan wasu mutane 25 sun bace, haka kuma yawan mutanen da suka ji rauni ya kai 12211. Ban da wannan kuma, mutane da yawansu ya kai kimanin miliyan 1.99 daga gundumomi 115 na birane da yankuna 19 suna fama da wannan bala'in a yanzu. A wani labarin kuma, hukumar kula da girgizar kasar ta kasar Sin ta ba da labari cewa, bisa bayanin da aka samu, an ce, an samu wassu girgizar kasa da suka biyo bayan babbar girgizar kasar har sau 3244, cikinsu yawan girgizar kasa da karfinsu ya wuce maki 3 sun kai sau 100.

A ranar Litinin 22 ga wata, hukumar kula da jin dadin jama'a ta lardin Sichuan da ke kasar Sin ta bayyana cewa, yanzu, an shirya kayayyakin ceton mutane zuwa yankunan da bala'in ya shafa sosai, amma, sakamakon dalilin sufuri, an samu wahala wajen sufurin kayayyakin ceto zuwa yankunan da bala'in ya shafa, haka kuma, a ranar 22 ga wata, kungiyar ceton jama'a ta kasar ta tura ayarori 5 don ceton mutane.

A sa'i daya kuma, sojojin sama sun tura jiragen sama masu saukar ungulu zuwa yankunan da bala'in ya shafa don kai kayayyakin ceto zuwa wurin, a ranar 22 ga wata, kwamitin kula da kiwon lafiya da tsara shirin haihuwa na Sin ya tura kungiyoyin kwararru zuwa yankunan da bala'in ya shafa.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China