in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Girgizar kasa da ta fadawa gundumar Lushan da ke lardin Sichuan a kasar Sin ta yi sanadiyyar mutuwar mutane 192
2013-04-23 11:07:08 cri

Bisa labarin da hedkwatar ba da umurni cikin gaggawa ta gwamnatin jama'ar lardin Sichuan dake kasar Sin ta bayar, an ce, ya zuwa ranar 22 ga wata da karfe 6 na yamma, girgizar kasa mai karfi maki 7 da ta fadawa gundumar Lushan ta yi sanadiyyar mutuwar mutane 192, baya ga wasu 23 da suka bace, haka kuma yawan mutanen da suka ji rauni ya kai 11470, cikinsu wasu 968 sun ji raunuka masu tsanani.

A ranar 22 ga wata, a birnin Beijing, yayin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ke karbar takardun kasa, da sabbin jakadun kasashe 9 da ke kasar Sin suka mika masa, cikinsu har da na sabbin jakadun kasashen Pakistan, Sudan da Philippines, Mr. Xi ya bayyana cewa, a madadin gwamnatin Sin da jama'ar kasar, ya yaba wa goyon baya da kasashen duniya suka nuna wa kasarsa, wajen yaki da bala'in girgizar kasa da aikin ceton jama'a. A cewarsa, yanzu, ana gudanar da aikin ceton jama'a yadda ya kamata.

A wannan rana, a nan birnin Beijing, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying, ta bayyana cewa, kasar Sin ta jinjina goyon baya da jaje, da kasashen duniya suka nuna wa gwamnatin kasar Sin da jama'arta bayan da girgizar kasa ta fada wa gundumar Lushan da ke lardin Sichuan a kasar. Ganin yanayin da ake ciki a wuraren da bala'in girgizar kasar ya shafa na da wahalar shiga, kuma kasar Sin na da kwarewa wajen ceton mutane da samar da isassun kayayyaki, shi ya sa, yanzu ba a bukatar taimako daga kasashen waje.

Mataimakin direkta na hukumar kula da harkokin jin dadin jama'a na lardin Sichuan Chen Kefu, ya bayyana cewa, yanzu, ana gaggauta samar da kayayyakin tallafi zuwa wuraren da bala'in ya shafa domin aikin ceton mutane. Haka kuma, ana iya tabbatar da samun kayayyakin masarufi a yankunan.

Yanzu akwai likitoci 11220 a wuraren da bala'in ya ritsa da su, kuma ya zuwa ranar 22 ga wata da karfe 3 da rabi na yamma, hukumar kiwon lafiya ta lardin Sichuan ta ceci mutanen da yawansu ya kai 10579, cikinsu har da 4312 wadanda tuni suka samu waraka. Ya zuwa yanzu, ba a gano barkewar annoba, ko matsalar kiwon lafiya a wuraren da bala'in ya shafa.

Ya zuwa ranar 23 ga wata da karfe 6 na safe, an samu karin girgizar kasa da suka biyo bayan babbar girgizar kasar har sau 3244, cikinsu yawan girgizar kasa da karfinsu ya wuce maki 3 sun kai sau 100.(Bako)

 

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China