Muddin ana so a kawar da zazzabin cizon sauro, wato malariya daga Najeriya, wajibi ne jama'a da gwamnatin kasar dake yammacin Afirka su yi aiki tare wajen tabbatar da lafiyar muhalli, ba wai kawai a dogara kan shan magani kadai ba don samun kariya daga cutar, in ji wani babban jami'in kiwon lafiya.
Okechukwu Ezekwesili, wanda shi ne shugaban sashen dakin bincike na cibiyar yaki da cutar malariya a asibitin kawancen kasar Sin da Najeriya dake Abuja, ya bayyana wa kamfanin dillancin labaran kasar Sin, Xinhua yayin wata hira cewa, ko da yake gwamnatoti a dukkan matakai suna samar da magunguna da ragar kare sauro ga jama'a, ana iya samun kariya daga wannan cuta idan aka tsabatce muhalli ta hanyar share kwalbatoci da magudanun ruwa.
Ya ce, Najeriya babbar kasa ce dake bukatar kara himma wajen tsabtace muhalli, idan ma ana bukatar karin masu share muhalli ne, to wajibi a yi hakan kafin a fara tunanin samar da magunguna da kuma ragar sauro.
Duk da cewa kasar ta Najeriya na ware dalar Amurka biliyan uku wanda ya yi daidai da kudin kasar naira biliyan 480, don yaki da cutar ta malariya a kowace shekara, mutane sama da dubu 300, mafi yawansu yara kanana na mutuwa sakamakon wannan cuta a kowace shekara a kasar.
A fadar ministan lafiya na kasar Onyebuchi Chukwu, yaro guda na mutuwa kowane minti daya sakamakon cutar a Najeriya, inda hakan ya sa kasar ita ce ke da mafi yawan masu cutar a duniya.
Ezekwesili ya ce, za'a iya shawo kan wannan lamari idan Najeriya ta yi koyi da kasar Sin da ma sauran kasashe masu ci gaba ta hanyar kara himma kan yaki da cutar malariya, wacce cuta ce da sauro ke yadawa.
Ya ce, a kiyasance, mutane a kalla 150 ne ke zuwa asibitin kawancen kasar Sin da Najeriya dauke da cutar malariya don neman magani, kuma ana iya samun wannan adadi ko fiye dake zuwa sauran asibitoci a birane da kauyuka don karbar maganin cutar a kowace rana a fadin kasar.(Lami)