in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya na bukatar wani sabon shirin yaki da cutar kanjamau
2013-04-23 10:41:02 cri

Shugaban tarayyar Najeriya Goodluck Jonathan ya umurci kwamitin kasa na yaki da ciwon Sida (NACA) a ranar Litinin da ya fitar da wani sabon shirin da zai taimaka wajen kawar da Sida.

A yayin da yake ganawa da darektan asusun MDD kan cutar Sida, cutar tari da zazzabin cizon sauro, mista Mark Dybul, shugaba Jonathan ya bayyana cewa, wannan shiri zai bullo da tsare-tsare masu muhimmanci da fayyace nauyin dake wuyan dukkan masu ruwa da tsaki da kuma sakamakon da ake bukata.

Ya kamata a cimma wata dubarar dake kunshe da matakai daban daban domin kawar da cutar zazzabin cizon sauro, in ji shugaban Najeriya tare da bayyana cewa, Najeriya na nuna godiya kan samun jarin kasa da kasa, musammun ma na gungun kasashen G8 wajen yaki da cutar kanjamau da sauran cututtuka.

Haka zalika, shugaban Najeriya ya jaddada niyyar kasarsa na cigaba da yin hadin kai tare da asusun duniya da kawar da cutar shan inna a kasar Najeriya nan da shekarar 2015. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China