Gwamnan jihar Borno a Najeriya Alhaji Kashim Shettima ya ziyarci garin Baga dake kan iyaka inda mutanen 185 suka hallaka sakamakon arangama da masu tsatsauran ra'ayin addinin nan na Boko Haram suka yi ma jami'an tsaro, hakan kuma ya haifar da lalata gidaje sama da 2000, sannan akwai baburan hawa fiye da 486 da aka kone su.
A lokacin wannan ziyarar jaje da duba adadin barna da hasarar lokacin fadan na ranar Juma'ar makon jiya, mai garin na Baga Malam Ali wanda ya zagaya da gwamnan ya bayyana cewar, 'yan kungiyar Boko Haram ne suka yi wannan taho mu gama da jami'an tsaro, abin da ya shafi mazauna garin tare da kawo asarar rayuka da dukiyoyi, ya zama daya daga cikin munanan hare-hare da suka auku tun bayyanar kungiyar a arewacin Nigeriya a 2009.
Wannan hari dai ya zo kwanaki uku da shugaban kasar Goodluck Jonathan ya kafa kwamitin sulhu da yi ma 'yan kungiyar afuwa domin a samar da wani yanayi na zaman lafiya a kasar dake yammacin Afrika.(Fatimah)