A ranar Litinin, magatakardan MDD Ban Ki-Moon ya ce, ya girgiza tare da nuna bakin ciki matuka dangane da rikicin da ya auku a arewa maso gabashin kasar Najeriya wanda ya yi sanadin salwantar rayuka a kalla 185, inda kuma ya yi kira ga masu tsatsauran ra'ayi su daina kai hari.
Wata sanarwar da mai magana da yawun magatakardan MDD ya bayar ta nuna cewa, babban sakataren na bakin cikin dangane da yawan mutane da aka hallaka da kuma gidaje da aka lalata sakamakon arangama tsakanin dakarun soji da masu tsatsauran ra'ayi a garin Baga na jihar Borno dake arewa maso gabashin Najeriya a ranar 19 da 20 ga watan Aprilu.
Ban ya yi ta'aziyya ga iyalan wadanda suka mutu, ya kuma yi kira ga masu tsatsauran ra'ayi su dakatar da kai hari, in ji sanarwar.(Lami)