Shugaban Najeriya Dr. Goodluck Jonathan ya bayyana zargin da ake yiwa gwamnatinsa, na tsunduma cikin ayyuka masu alaka da cin hanci da rashawa, a matsayin wani zargi maras tushe ko makama.
Shugaban wanda ya yi wannan tsokaci yayin bikin rattaba hannu kan wasu takardu, da suka shafi sauye-sauye ga sashen lantarkin kasar, wanda aka gudanar a fadar gwamnatin Najeriyar dake birnin Abuja, ya kara da cewa, gwamnatinsa na iyakacin kokarinta, wajen ganin an magance matsaloli masu alaka da cin hanci da rashawa, a dukkanin sassan ayyukan hukuma. Bugu da kari, Jonathan ya ce, a yanzu haka kwalliya ta fara biyan kudin sabulu, ba kamar yadda a cewarsa, wasu ke yayata habakar matsalar ba.
Daga nan sai shugaba Jonathan ya jaddada aniyar gwamnatinsa, don gane da daukar dukkanin matakan da suka kamata, domin kawo karshen matsalolin karancin wutar lantarki dake addabar kasar.
A 'yan kwanakin baya ne dai sakataren wajen kasar Amurka John Kerry, ya mikawa majalissar dokokin kasar Amurka wani rahoto, wanda ke nuna yadda matsalar cin hanci da rashawa, ke ci gaba da yiwa daukacin sassan hukuma a Najeriyar kamun kazar kuku.(Saminu)