in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Majalisar dattijan Najeriya ta fara bincike kan kisan mutane a garin Baga
2013-04-24 10:04:56 cri

A ranar Talata 23 ga watan nan ne majalisar dattijan Najeriya ta fara gudanar da wani bincike, kan musabbabin kisan mutane da yawansu ya kai 185, yayin wata musayar wuta da ta auku, tsakanin jami'an rundunar sojin kasar da kuma wasu gungun mahara dauke da makamai. Musayar wutar wadda ta jikkata mutane da dama, baya ga wadanda suka rasa rayukansu, ta auku ne a karshen makon da ya gabata, a garin Baga dake arewacin jihar Borno.

Shugaban majalisar David Mark ne ya ba da umarnin aiwatar da binciken, ga kwamiti mai lura da harkokin tsaro, da 'yan sanda, bayan da 'dan majalisar mai wakiltar mazabar arewa maso gabashin jihar ta Borno Sanata Maina Lawan, ya gabatar da kudiri don gane da hakan.

David Mark ya ce, koma waye ke da alhakin kisan wadannan mutane, hakika ya aikata gagarumin laifi, don haka kwamitin majalisar zai tabbatar da gaskiyar yadda wannan balahira ta auku, ko da yake ya ce, ba za a tafka mahawara, kan ko wannan batu na da alaka da kisan kiyashi ko kuwa a'a ba, kasancewar tuni sashen zartaswar kasar ya kafa wani kwamiti da zai gudanar da bincike kan hakan.

An dai bai wa kwamitin majalisar dattijai wa'adin makwanni biyu, domin kammala aikinsa, ya kuma gabatar da sakamako ga zauren majalisar. Daga bisani majalisar ta yi shiru na minti guda, domin girmamawa ga wadanda wannan al'amari ya ritsa da su.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China