in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Majalissar wakilan Najeriya ta bukaci gudanar da bincike kan kisan mutane a garin Baga
2013-04-25 10:02:13 cri

Majalissar wakilan Najeriya ta bukaci sashen zartaswar kasar, da ya kafa kwamitin bincike na musamman, wanda zai gudanar da sahihin bincike kan kisan mutane kimanin 185, da aka yi a garin Baga, na jihar Borno, dake arewa maso gabashin kasar, yayin wani dauki ba dadi tsakanin magoya bayan kungiyar nan ta Boko Haram, da dakarun sojin kasar, da ya auku a karshen makon da ya gabata.

Wata sanarwa daga majalissar, wadda kamfanin dillancin labarun kasar Sin Xinhua ya samu kwafi, ta bayyana bukatar kwamitin da ya tantance musabbabin rasuwar mutanen, tare da kira ga mambobin kungiyar ta Boko Haram, da su rungumi shirin afuwa da gwamnatin tarayya ta bullo da shi.

Har ila yau, majalissar ta wakilai, ta bukaci hukumar ba da agajin gaggawa ta kasar NEMA, da ta samar da kayayyakin tallafi ga al'ummar da wannan balahira ta aukawa.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China