in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana ci gaba da aikin ceto a gundumar Lushan ta lardin Sichuan a kasar Sin sakamakon girgizar kasa
2013-04-22 15:30:41 cri

Ya zuwa karfe 2 na maraicen ranar jiya Lahadi 21 ga wata, yawan mutane da girgizar kasa mai karfin digiri 7 bisa ma'aunin Richter ta galabaitar da su a gundunar Lushan ta lardin Sichuan a kasar Sin sun kai fiye da miliyan 1.5, mutane 186 sun mutu, yayin da 21 suka bace, sannan kuma mutane 11,393 suka raunana. Ya zuwa yanzu dai, gwamnatin ta yi kokarin tsugunar da mutane da wannan hadari ya shafa da yawansu ya kai dubu 171.

Mataimakin firaministan kasar Sin Wang Yang ya ci gaba da ba da jaroranci ga aikin ceto a wurin, kuma ya nemi bangarori daban-daban da su yi iyakacin kokarin su domin gudanar da aikin ceto, ta yadda za a ceci dukkan mutanen da suke raye a baraguzan gine-gine.

Ban da haka, baitulmalin gwamnatin tsakiya ya kebe kudin tallafi Yuan biliyan 1 cikin gaggawa domin ba da taimako ga aikin ceto da ba da kulawa da mutane da suka firgici. Ya zuwa yanzu, sojin kasar Sin, jami'an tsaro masu dauke da makamai da ma'aikatan kwana-kwana suna kokarin gudanar da aikin ceto a wurin.

Bayan abkuwar wannan bala'i, kasashen duniya sun maida hankulan su sosai kan lamarin,tare da jajantawa ta hanya daban-daban tare da bayyana aniyar su na bada taimako. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China