in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
(Sabunta)Mutane fiye da 200 sun rasa rayukansu sakamakon bala'in girgizar kasa a Lushan
2013-04-21 20:23:18 cri

Bisa kididdigar da hukumar kula da harkokin jama'ar lardin Sichuan ya yi da karfe 5 na yammacin ranar 21 ga watan nan da muke ciki, an ce, mutane 184 sun rasa rayukansu, yayin da mutane 24 suka bace, baya ga mutane 11826 da suka ji rauni a sakamakon bala'in girgizar kasa da ya auku a gundumar Lushan na yankin birnin Ya'an dake lardin Sichuan. Bisa labarin da aka bayar, an ce, bayan da firaministan kasar Sin Li Keqiang ya yi bincike kan halin da ake ciki a yankin, ya kuma shirya aikin bada ceto, ya koma birnin Beijing a wannan rana da yamma. Kafin nan ya nanata bukatar sanya aikin ceto mutane a gaban kome. A halin yanzu, an bada jinya ga dukkan mutanen da suka ji rauni a sakamakon bala'in a garin Lushan, an kuma ci gaba da zirga-zirgar ababan sirifi a hanyoyi da dama dake yankin da bala'in ya aukawa.

Bayan abkuwar girgizar kasar a garin Lushan dake kasar Sin, kasashen duniya da yawa sun sanya lura sosai kan halin da ake ciki a yankin, musamman batun ayyukan bada ceto da gwamnatin kasar Sin ta gudanar. Kasashen duniya da dama sun bayyana cewa, idan akwai bukata, suna da burin bada gudummawa ga yankin mai fama da bala'i. A ranar 21 ga wata, kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin Qin Gang ya bayyana cewa, gwamnatin kasar Sin da jama'arta suna godiya ga kasa da kasa domin nuna jajantawa da goyon baya da sukewa kasar ta Sin. A halin yanzu, an tura cikakkun masu bada ceto da bada jinya zuwa yanki mai fama da bala'in, domin tabbatar da samar da kayayyakin taimako. Har ila yau, sakamakon rashin kyaun yanayin hanyoyin motoci da sadarwa, ba a bukatar kasashen duniya su tura rukunin ayyukan ceto da kayayyakin taimako zuwa yankin a wannan lokaci. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China