Li Keqiang, firaministan kasar Sin wanda ke ba da jagoranci ga aikin ceto a gundumar Lushan, inda aka samu bala'in mafi tsanani, ya jaddada cewa, dole ne a sanya aikin ceto mutane a gaban kome. Sannan ya alkawarta cewa, gwamnati za ta taimakawa jama'a wadanda bala'in ya aukuwa wajen sake gina gidajensu.
Bisa labarun da muka samu, an ce, bayan aukuwar bala'in girgizar kasa a gundumar Lushan, kasashen duniya, kamar su Amurka, Rasha, Japan, Bribaniya, Faransa, Cuba da dai sauransu sun nuna jajantawa gwamnatin kasar Sin, inda suka yabawa matakan ceton jama'a da gwamnatin kasar Sin ta dauka a kan lokaci, kuma suka bayyana cewa, suna fatan za su iya ba da tallafi ga jama'ar da suke fama da radadin wannan bala'in. (Sanusi Chen)