in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane 56 sun mutu sakamakon girgirzar kasa da ta auku a birnin Ya'an na lardin Sichuan na kasar Sin
2013-04-20 14:28:16 cri

Bisa labarin da aka samu, an ce, mutane 56 sun mutu sakamakon girgizar kasa da ta auku a birnin Ya'an na lardin Sichuan na kasar Sin. Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bukaci a yi iyakacin kokari don ceton jama'a da wannan bala'in ya shafe su. Firaministan kasar Li Keqiang kuma ya riga ya tashi daga birnin Beijing cikin jirgin sama zuwa yankin da bala'in ya auku don ba da jagoranci ga aikin ceto.

Tashar Intanat ta watsa labaru kan girgizar kasa ta lardin Sichuan ta ba da labarin cewa, da misalin karfe 8 da minti 2 na safiyar yau, aka yi girgizar kasa wadda karfinta ya kai digiri 7 bisa ma'aunin Richter a gundumar Lushan ta lardin Sichuan.

Bayan abkuwar girgizar kasar, kwamitin tsakiya na Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin da majalisar gudanarwa ta kasar sun dora matukar muhimmanci kan batun. Shugaba Xi Jinping da Firaminista Li Keqiang sun ba da muhimman sanarwa daya bayan daya, inda suka bukaci a fahimci halin da ake ciki a yankunan da ke fama da bala'in, sannan a mayar da ceton jama'a a gaban dukkan ayyuka, a kokarin rage yawan mutanen da za su mutu ko jikkata sakamakon bala'in.

A sa'i daya kuma, ya kamata a kara sanya ido kan bala'in girgizar kasar don magance matsaloli na mataki na biyu sakamakon girgizar. Bugu da kari ya kamata a mai da hankali kan aikin tsugunar da jama'a masu fama da bala'in don tabbatar da zaman karko a yankunan.

Ban da wannan kuma, 'yan kwana-kwana a lardunan da ke makwabtaka da lardin Sichuan a shirye suke don gudanar da aikin ceto, sannan ma'aikatan kwana-kwana 309 da motoci masu kula da aikin kwana-kwana 49 da ke sauran yankunan lardin Sichuan sun nufi yankin da ke fama da bala'in don aikin ceto.

Haka zakila, an tura 'yan sanda masu kwantar da tarzoma 3900 zuwa yankin da aka yi girgizar kasar, inda kawo yanzu dai 2600 daga cikinsu sun riga sun fara aikin ceto.(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China