in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yanzu ceton rayukan mutane yana gaba da kome, in ji firaministan kasar Sin
2013-04-21 10:17:16 cri

Ranar 20 ga wata da dare, a gundumar Lushan ta birnin Ya'an a lardin Sichuan na kasar Sin, Li Keqiang, firaministan kasar ya ci gaba da tsara ayyukan rage radadin bala'in girgizar kasar da ta auku a wurin, inda ya jaddada cewa, yanzu aiki mafi muhimmanci da ake yi a lardin na Sichuan shi ne rage radadin bala'in da ya auka wa yankin, tare da ceton rayukan mutane.

Mista Li ya kara da cewa, wajibi ne a ba wa wadanda suka jikkata jinya yadda ya kamata, a kai wadanda suka ji munanan raunuka asibitocin da ke wuraren da bala'in bai shafa ba cikin gaggawa, a kokarin rage yawan mutuwar mutane da yawan wadanda za su nakasa sakamakon bala'in.

Ya zuwa ranar 21 ga wata da karfe 9 da rabi na safe, mutane 179 suka rasa rayukansu sakamakon girgizar kasar, ciki har da 164 a birnin na Ya'an.(Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China