Li ya shiga jirgi mai saukar ungulu zuwa inda girgizar kasar ta auku a Lushan cikin garin Ya'an bayan da ya isa Sichuan. Ya yi kiran wata ganawa da misalin karfe 6 na yamma, inda ya ba da umarni a bude hanyar zuwa garin Baoxing da ta toshe kana ya bukaci masu aikin agajin su yi gaggawa.
Bayan abkuwar bala'in, ma'aikatar albarkatun kasa ta kasar Sin ta kaddamar da tsarin warware matsalolin gaggawa na mataki na uku ba tare da bata lokaci ba, daga baya kuma ta daga matsayin zuwa na farko. Sannan an fara ayyukan tantance hasara da aka yi sakamakon bala'in, da kuma yanayin kasa wajen yin ayyukan farfadowa bayan bala'in.
Haka kuma bisa labarin da muka samu daga wajen 'yan sanda masu kwantar da tarzoma, an ce, yawan 'yan sandan da suka shiga yankin da bala'inn ya shafa don aikin ceto ya karu zuwa 4510, kana an aika da manyan motoci masu aikin injiniya 60 don aikin ceto.(Lami, Kande Gao)