Firaministan kasar Sin Li Keqiang ya sauka a filin jirgin sama na Qionglai da ke lardin Sichuan don ba da aikin jagoranci a inda girgizar kasa ta auku a Ya'an na lardin, sannan akwai wasu ma'aikata da za su shiga jirgi mai saukar ungulu don zuwa yankin da bala'in ya shafa.
Bayan da jirgin ya tashi daga Beijing, Li Keqiang ya kira taro a cikin jirgin, inda ya ba da umurni kan yadda za a gudanar da ayyukan ceton mutane da bala'in ya shafa. Ya jaddada cewa, ya kamata a mayar da jama'a a gaban kome, kuma a yi namijin kokarin don ceton mutanen da suka samu kansu cikin bala'in cikin sa'o'i72.
Bisa sabuwar kididdigar da hukumar kula da ayyukan da suka shafi girgizar kasa ta kasar Sin ta bayar, an ce, kawo yanzu dai, girgizar kasar ta haddasa mutuwar mutane 100, yayin da wasu fiye da 2000 sun jikkata. Yanzu kuma ana ci gaba da kidayar yawan mutanen da suka mutu da wadanda suka jikkata sakamakon bala'in.(Kande Gao)