in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
'Yan wasan kwaikwayon Nijeriya a Beijing suna fatan alheri ga masu fama da girgizar kasa a lardin Sichuan na Sin
2013-04-20 20:17:00 cri
A ranar Asabar 20 ga wata a nan birnin Beijing, bayan samun labarin mutuwa da jikkatar mutane da yawa a sakamakon abkuwar bala'in girgizar kasa mai tsanani a gundumar Lushan ta lardin Sichuan na Sin, 'yan wasan kwaikwayon Nijeriya 6 dake aikin sanya murya ga film din Soyayyar Matasan Beijing, sun nuna jimami ga wadanda bala'in ya shafa.

Shahararriyar 'yar wasan kwaikwayon Nijeriya, Fatima Musa ta girgiza sosai bayan jin wannan labari, har ma ta yi kuka bayan da ta ji cewa, mutanen Sin da yawa sun yi hasarar iyalai da gidaje. Fatima Musa ta bayyana fatanta cewa, mazauna wurin za su yi nasarar yaki da wannan bala'i, tare da sake kafa gidajensu cikin sauri.

Dan wasan kwaikwayon Nijeriya, Muhammad Yahaya shi ma ya nuna jinjinawa ga wadanda ke fama da bala'in a lardin Sichuan, tare da fatan iyalansu za su sami lafiya. Ya ce, girgizar kasar da ta abku a shekarar 2008 a Wenchuan ta nuna cewa, gwamnatin kasar Sin tana kulawa da jama'ar kasar yadda ya kamata, tare da ba da agaji ga masu fama da bala'in a fannoni daban daban. Yana son yin addu'a domin wadanda suka mutu da wadanda suka jikkata a sakamakon bala'in.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China