Jami'in ya nuna cewa, wurare daban daban da hukumomin da abin ya shafa na kasar Sin sun dauki matakai a shekara ta 2010 don inganta abinci, inda suka yi yaki da harkokin aikata laifuffukan da suke da nasaba da samarwa da sayar da abinci maras inganci ko gurbatacce, kana da yanke hukunci ga wasu masana'antun da suka karya doka. Kuma wannan jami'i ya kara da cewa, a bara, an tono lamarin karya doka fiye da dubu 130 a fannonin shuke-shuke da kiwon dabbobi da sarrafa abinci da cinikayya kana da ba da hidima ta fuskar abinci, kuma an kama mutanen da ake tuhumarsu da wadannan laifuffuka 248.
A waje daya kuma, wannan jami'i ya ce, ko da yake an samu ci gaba a wannan fanni, amma ayyukan da suka shafi ingancin abinci na kasar Sin ba su da tushe mai inganci. Sakamakon kasancewar dimbin masu samarwa da masu sayar da abinci suka a fannoni daban daban da kuma bukatun da ake da shi na samar da abinci kimanin kilogram biliyan daya a ko wace rana, halin da kasar Sin ke ciki ta fuskar ingancin abinci na da tsanani.(Kande Gao)