in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta yi shirin warware matsalar abinci cikin shekaru 3 masu zuwa
2012-07-04 12:09:59 cri
Bisa labarin da shafin Internet na gwamnatin Sin ya bayar, an ce, shirin tabbatar da ingancin abinci da majalisar gudanarwa ta Sin ta bayar a kwanan baya, ya bayyana burin kasar Sin game da tabbatar da ingancin abinci, nan da shekaru 3 masu zuwa, Sin za ta kyautata ingancin abinci don samun sakamako mai gamsarwa, kuma za a yaki aikata wasu laifuffuka game da matsalar abinci.

Ban da wannan kuduri, ya kuma bayyana cewa, nan da shekaru 5 masu zuwa, za a kafa tsarin sa ido game da inganci abinci da dokokin da suka shafi ingancin abinci, ta yadda za a karfafa ingancin abinci da ake sayarwa mutane, da kara tunaninsu game da ingancin abinci, ta yadda, bangarorin daban daban za su shiga cikin wannan aiki, domin inganta kyautatuwar abinci a cikin kasa baki daya.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China