A yayin taron ganawa da manema labaran da aka shirya a ranar Litinin 13 ga wannan wata, shugaban hukumar kula da ingancin abinci ta kasar Sin Su Zhi ya sanar da shirin bunkasa tattalin arzikin kasar Sin na shekaru biyar biyar na sha biyu kan ma'aunin ingancin abinci inda ya bayyana cewa, kasar Sin za ta kara mai da hankali kan aikin kyautata ingancin abinci, ya zuwa lokacin da za a kammala aikin gudanar da shirin shekaru biyar biyar na sha biyu a kasar wato shekara ta 2015, za a cimma burin tsara tsarin ma'aunin ingancin abinci mai biyan bukatun lafiyar jikin jama'a wanda zai dace da tsarin musamman na kasar Sin.
Kan wannan batu, Su Zhi ya kara da cewa, shirin da aka tsara ya gabatar da burin aikin da za a cimma a fannoni hudu wadanda ya hada da: na farko, kyautata ma'aunin ingancin abinci na yanzu tare da kafa ma'aunin ingancin kayayyakin noma da abinci yadda ya kamata, na biyu, hanzarin kafa da kuma kyautata ma'aunin ingancin abinci na matsayin kasa tare da amfaninsa ta hanyar kimiyya, na uku, kyautata tsarin tafiyar da ma'aunin ingancin abinci a kasar tare da hukumomin da abin ya shafa, na hudu, kara karfafa aikin aiwatar da tsarin da aka tsara tare da sa ido kan sassa da hukumomi daban daban da abin ya shafa a kasar domin su tabbatar da tsarin ma'aunin lami lafiya.(Jamila)