Mataimakin firaministan kasar Sin kuma darektan kwamitin inganta abinci na majalisar gudanarwa ta kasar Li Keqiang ,a ranar 8 ga wata ,ya jaddada cewa, ya kamata a tsaurara yanke hukunci kan laifin rashin inganta abinci, domin kyautata tsarin duba wannan aiki da kara ingancin abinci.
A wannan rana, Li Keqiang ya shugabanci babban taro na kwamitin inganta abinci na majalisar gudanarwa ta kasar Sin, inda aka saurari rahoton da membobin ofishin kula da ingancin abinci da kwamitin inganta abinci na majalisar gudanarwa ta kasar Sin suka bayar, kuma an tattauna kan shirin manyan ayyukan kara ingancin abinci na shekara ta 2012.
A wurin taron, an kayyade cewa, dole ne gwamnatocin jahohi daban daban na kasar Sin su ci gaba da duba aikin tabbatar da ingancin abinci da kafa tsarin kula da lamarin rashin ingancin abinci da tabbatar da isassun ma'aikata da kudi da kuma na'urori domin kyautata aikin sa ido kan ingancin abinci. (Lami)