Akwai kananan kabilu 10 da ke bin addinin Musulunci a kasar Sin, kuma yawan Musulmi a kasar Sin ya zarce miliyan 22, sabo da lardunan daban daban na kasar Sin ba su cimma matsaya guda ba game da ka'idojin abincin halal, yanzu, babu wani tsarin tabbatar da abincin halal a kasar. A shekarar 2009, jihar Ningxia ta aiwatar da ka'idar tabbatar da abincin halal ta jihar Ningxia ta kabilar Hui mai cin gashin kanta, kuma wannan ka'ida ita ce ka'ida kawai da ake bi a wadannan larduna da jihohi biyar kafin tabbatar da sabuwar ka'ida.
An tsara Ka'idojin abincin halal na larduna 5 a kasar Sin bisa ka'idar abincin halal na jihar Ningxia ta kabilar Hui mai cin gashin kanta, tare da jin ra'ayoyin kungiyoyin addini da masu sa ido game da abinci, don tsara wannan ka'idoji tare.(Bako)