Kasar Sin za ta tsara da kuma kyautata ka'idoji 1000 wajen tabbatar da ingancin abinci
A ranar 12 ga wata, bisa shirin raya abinci da masana'antu cikin lokacin samun bunkasuwa a karo na 12 na shekaru biyar-biyar da kwamitin yin gyare-gyare da samun bunkasuwa na Sin da ma'aikatar kula da harkokin masana'antu da sadarwa ta kasar suka bayar, an ce, ya zuwa shekarar 2015, kasar Sin za ta tsara da kuma kyautata ka'idoji 1000 wajen tabbatar da ingancin abinci, kuma za ta kafa wani tsari ne game da wannan, don kokarin kyautata abinci da ingancinsu zai kai sama da kashi 97 cikin 100 yayin da ake dubawa, ta hakan za a kara gamsar da jama'a game da ingancin abinci.
Haka kuma, shirin ya bukaci da a bi bukatun sa ido game da ingancin abinci da tantance hadarin abinci, a samar da na'urorin tantance ingancin abinci, musamman ma a inganta hukumomi na wurare daban daban da su kyautata kwarewarsu wajen sa ido game da ingancin abinci, da nuna goyon baya game da samar da na'urorin tantance ingancin abinci da kansu, da horar da ma'aikata masu sa ido, don tabbatar da sassan daban daban na kasar Sin wajen sa ido game da ingancin abinci da samar da na'urori wajen sa ido, har ma da ba da kudade wajen horar da kwararru.(Bako)