Sa'an nan, a wajen wata cibiyar sa ido kan ingancin abinci da ke birnin Tianjin, shugaba Hu ya furta cewa, jama'a kan baiwa abinci muhimmanci, kana aikin da ya shafi abinci wanda ke da matukar muhimmanci shi ne tabbatar da ingancinsa. Kokarin tabbatar da ingancin abinci ya kasance wani muhimmin aikin da ya shafi lafiyar jama'a da rayuwarsu. Don haka, cibiyar sa ido da binciken ingancin abinci, a matsayinta na wata babbar hukuma mai kula da ingancin abinci, tilas ne ta nace ga bin dokar ingancin abinci, da nuna kulawa ga jama'a, kana ta kara karfin sa ido, don tabbatar da ganin jama'a suna more duk nau'in abincin da suke so ba tare da damuwa kan ingancinsa ba. (Bello Wang)