in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin Faransa sun kashe dakaru sama da 10 a yankin arewacin Mali
2013-03-22 16:24:26 cri
A ranar 21 ga wata, hedkwatar rundunar tsaro ta sojojin Faransa ta ba da sanarwa cewa, a ranar 20 ga wata da tsakar dare, sojojin Faransa da na kasar Mali sun kashe dakaru masu adawa da gwamnatin kasar Mali sama da 10 a yankin arewacin kasar.

Hedkwatar rundunar tsaro ta sojojin Faransa ta bayyana cewa, a ranar 20 ga wata da dare, wani gungun dakaru masu adawa da gwamnatin Mali sun yi yunkurin shiga filin jirgin sama na Timbuktu da ke yankin arewacin kasar, to, amma sojojin Faransa da na Mali dake hake a wurin sun dakile yunkurin tare da mayar da martani, inda bangarorin biyu suka yi musayar wuta har zuwa safiyar ranar 21 ga wata. Wani soji na gwamnatin Mali ya mutu, kana wasu sojojin kasar a kalla 3 sun jikkata.

A wannan rana, ministan harkokin waje da hadin kan kasashen Afrika na kasar Chadi Moussa Faki Mohamoud ya bayyana cewa, sojojin Chadi da na Faransa, sun kammala aikin cafke dakaru masu makamai da yawansu ya kai kashi 70 cikin 100 a yankin faffadan tsaunin Ifo Las da ke arewa maso gabashin kasar, inda ya ci gaba da bayyana cewa, sojojin Chadi za su ci gaba da kasancewa a Mali, don shiga cikin rundunar kiyaye zaman lafiya ta M.D.D.

A wata sabuwa kuma, a ranar 21 ga wata, majalisar harkokin kasashen waje ta Amurka ta sanar da cewa, za ta kakaba takunkumi kan kungiyar Ansar al-Dine da ke kasar Mali, kana za ta hana jama'ar Amurka nuna goyon baya ga kungiyar, tare da hana cire kudaden da ta ajiya cikin harabar da Amurka ke kulawa.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China