Mr. Fabius ya kuma bayyana cewa, zai ziyarci kasar ta Mali ran 5 ga watan Afrilun nan, don ganawa da manyan jami'an gwamnatin wucin gadin kasar Mali.
Ran 30 ga watan Maris, shugaban gwamnatin wucin gadin kasar Mali Dioncounda Traore, ya nada shugaba da kuma mataimakin shugaban kwamitin shawarwari da neman sulhun kasar. Kuma bisa shirin da gwamnatin ta gabatar, kwamitin zai kunshi mambobi 30, wadanda za su dukufa wajen nemen hanyoyin wanzar da sulhu, tsakanin bangarori daban daban da rikicin kasar ya shafa ta hanyar shawarwari. (Maryam)