An yi musayar wuta tsakanin rundunar sojin hadin gwiwar kasar Chadi da Faransa, da dakarun kungiyar 'yan tada kayar baya ta musulmi dake adawa da gwamnatin kasar Mali a ran 22 ga wata.
A ran 24 ga wata hukumar sojin Chadi ta tabbatar da cewa, cikin fadan da aka yi a ran 22 ga wata, an harbe 'yan ta'adda 93, da kuma lalata motocin soja 6, baya ga sojinta 23 da suka mutu ciki hadda wani hafsa, yayin da wasu 3 suka jikkata.
A ran 22 ga wata a babban tudun nan na Ifo Las dake arewa maso gabashin kasar ta Mali, an shiga mawuyacin halin yaki, inda sojin Faransa da Chadi suka fafata da rundunar 'yan adawar kasar ta Mali. Bayan harin da aka kai musu, sojin Chadi sun mayar da martani da luguden wuta, yayin da kuma sojin Faransa suka ba da taimako ta hanyar tura jiragen saman yaki.
Shugaban kasar Faransa Francois Hollande ya fadi a ran 23 ga wata cewa, yanzu an shiga matakin karshe na aikin soja da dakarun kasarsa ke yi a kasar Mali. Amma har ila yau wasu manyan jagororin 'yan tawayen dai na boye ne a wannan yanki, lamarin da ya wajabta bukatar ci gaba da kai samame daga sama domin murkushe su. (Amina)