Shafin Intanet na ma'aikatar tsaron kasar Faransa ya ba da wata sanarawa a ran 4 ga wata da dare, wadda ke cewa, sojin kasar sun harbe 'yan bindiga fiye da 40, yayin wani simame da rundunar ta kai a faffadan tsaunin Ifolas, dake arewa maso gabashin kasar Mali.
Cikin matakan sojan da sojojin Faransa suka dauka daga ranar 28 ga watan Fabrairu zuwa 4 ga watan da muke ciki sun kuma lalata motoci fiye da 10, da wata igwa, har ma sun kwace dimbin makamai da harsashi.
Sanarwar ta ce, a wani wurin dake kusa da birnin Gao, birni mafi girma a arewacin kasar ta Mali, sojin kasar Faransa da na Mali sun kwato wani kauye da 'yan bindiga suka mamaye, suka kuma harbe magoya bayan su sama da 40.
Hafsan sojin kasar Faransa janar Édouard Guillaud ya shedawa manema labaru na kasar a wannan rana cewa, sojin kasar sun gano wurare da ake kera makamai, ciki hadda wurare fiye da 50 da aka boye makaman a faffadam tsaunin Ifolas.
A cewarsa, daruruwan 'yan bindiga na ci gaba da boyewa a wannan yanki. (Amina)