Kwamitocin shirya rajistan masu zabe za su yi wani zaman taro nan ba da jimawa ba, in ji darektan hukumar fadin kasar Mali, mista Bassidi Coulibaly a ranar Talata a yayin wani taro a Bamako.
Zaben shugaban kasa zai gudana a cikin watan Yuli mai zuwa, a cewar hukumomin kasar. Dalilin haka ne kwamitocin dake da nauyin shirya takardun sunayen masu kada kuri'a za su yi wani zaman taro nan ba da jimawa ba, in ji mista Coulibaly tare da bayyana cewa, wannan ba zai yiwu ba idan babu ikon gwamnati a cikin wadannan yankuna uku na arewacin kasar Mali.
Hukumomin yankin Kidal za su kasance cikin gajeren lokaci cikin wannan yanki tare da taimakon rundunar sojojin kasar Mali tare da hadin gwiwar sojojin tawagar tallafawa kasar Mali ta MISMA, in ji mista Coulibal.
A yayin da yake tabo maganar kudaden da za su taimaka wajen shirya zabubuka, mista Coulibaly ya ce, sun tashe zuwa kudin Sefa biliyan 64, kuma gwamnatin kasar Mali za ta ba da biliyan 25 yayin da sauran kudaden za su fito daga kungiyoyi da kasashen dake tallafawa kasar Mali. (Maman Ada)